Mark 12

1Sai Yesu ya fara koyar da su da misalai. “Wani mutum ne ya yi gonar inabi ya shingen ta, ya haka ramin matse inabin, ya kuwa gina hasumayar tsaro. Ya ba wandansu manoma jinginar gonar, sa’an nan ya tafi wata kasa mai nisa. 2Da lokaci ya yi, sai ya aika masu wani bawansa domin ya karbi wadansu daga cikin amfanin gonar. 3Amma manoman suka kama shi, suka yin masa duka, suka kore shi hannu banza.

4Ya sake aikar wani bawan. Shi kuma suka raunata shi aka, suka wulakanta shi. 5Ya sake aiken wani. Shi kam, suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da wadansu da yawa, sun dodoki wadansu, suka kuma kashe wadansu.

6Yanzu dai yana da sauran daya tak, shine kaunatacen dansa. Daga karshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ai za su bashi girma. 7Amma manoman nan suka ce wa juna, “ai, wannan shine magajinsa, ‘ku zo mu kashe shi, gadon ya zama namu.”

8Sai suka kamo shi, suka kashe shi, suka jefar da shi bayan shinge. 9To, me mai gonar inabin zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba wadansu gonar.

10Ashe, ba ku karanta wannan nassi ba? cewa, ‘Dutsen da magina suka ki, shi ne ya zama mafi mahmimanci. 11Wannan daga Ubangiji ne, kuma ya yi dai dai a idanunmu.”’ 12Sai suka nemi su kama shi, don sun lura a kansu ne ya yi masalin, amma suka ji tsoron jama’a. Don haka suka kyele shi, suka tafi.

13Suka aika masa da wadansu farisiyawa da Heridiyawa, don su sa masa tarko da kalamai cikin maganarsa. 14Da suka zo, suka ce masa, “Malam, gaskiya kana koyar da maganar Allah sosai, ba ka nuna bambanci tsakani mutane, sai koyar da tafarkin Allah kake yi sosai. “Shin, mu biya haraji ga Kaisar, ko a a?” 15AmmaYesu ya gane munafuncinsu, ya ce masu, “Don me kuke gwada ni? ku kawo mani dinarin in gani.”

16Suka kawowa Yesu daya. Ya ce masu, “Kamar waye da kuma rubutun wanene? suka ce masa, “Na Kaisar ne.” 17Yesu ya ce, “to, ku ba Kaisar abinda yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah. Sai suka yi mamakinsa kwarai.

18Sai Sadukiyawa suka zo wurinsa, su dake cewa babu tashin matattu. Suka tambaya shi suka ce, 19“Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan dan’uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba da, lallai ne dan’uwan mutumin ya auri matar, ya haifa wa dan’uwansa ‘ya‘ya.’

20To an yi wadansu ‘yan’uwa maza guda bakwai, na farko ya yi aure, ya mutu bai bar ‘ya’ya ba. 21Na biyu kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba ‘ya’ya. Na ukun ma haka. 22Haka dai duk bakwai din, ba wanda ya bar ‘ya’ya. A karshe kuma ita matar ta mutu. 23To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai din nan sun aure ta”.

24Sai Yesu ya ce, “Ba saboda wannan dalili ne kuka yi kuskure ba, wato don ba ku san littafin ba, kuma ba ku san ikon Allah ba? 25Domin in an tashin daga matattu, ba a aure, ba a auraswa, amma sun zama kamar malaiku a sama.

26Amma game da mattattun da suka tashi, ashe, ba ku taba karantawa a littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa? “Ni ne Allah na Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu’? 27Ai, shi ba Allahn mattatu bane, amma na rayyayu ne. Hakika kun yi kuskure “.

28Sai wani malamin attuara ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu yana ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, “Wanne Umarni ne mafi girma dukka?” 29Yesu ya amsa yace, “mafi girma shine, ‘ku saurara ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji daya ne. 30Sai ka kaunaci Ubangiji Allah da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka da dukkan tunaninka, da dukkan karfinka. 31ta biyu itace, ‘ka kaunaci makwabcinka kamar kanka, Ba wata doka da ta fi wadannan.‘’

32Sai malamin attaura ya ce masa, “Hakika gaskiyarka malam, Allah daya ne, ba kuma wani sai shi. 33A kaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukkan hankali, da dukkan karfi, a kuma kaunaci makwabci kamar kanka, ai ya fi dukkan hadayu na konawa.” 34Da Yesu ya ga ya yi masa magana da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka nesa da mulkin Allah.” Bayan wannan kuma ba wanda ya sake tambayarsa wani abu.

35Yesu ya amsa a lokacin da yake koyarwa a Haikali, ya ce “Yaya malaman attaura suke ce wa Kristi dan Dauda ne? 36Domin Dauda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ubangiji ya ce wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na kaskantar da makiyanka’. 37Dauda da kansa ya kira shi ‘Ubangiji; To, ta yaya ya Almasihu zai zama Dan Dauda?” Babban taron jama’ar suka saurare shi da murna.

38A koyarwa sa Yasu ya ce, “ku yi hankali da malaman attaura, masu son yawo da manyan riguna, suna so a gaishesu a kasuwa, 39da kuma son wuraren zama masu daraja a haikali, da wurin bukukuwa. 40Sun kuma kwace gidajen gwauraye, da yin doguwar addu’a, don mutane su gani. Wadanan mutanen zasu sami hukunci mai tsanani.”

41Sai ya zauna a gaban akwatin baiko a Haikalin, yana duban yadda jama’a suke zuba kudi a ciki. 42Wadansu masu arziki da yawa suna zuba kudi masu tsoka. Sai gwauruwa mara abin hanu ta saka anini biyu a ciki akwatin baikon.

43Ya kira almajiransa, ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, abinda gwauruwa nan ta saka a akwatin baikon nan ya fi na sauran dukka. Su duk sun bayar daga yalwa tasu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta bada duk abinda take da shi.”

44

Copyright information for HauULB